Labarai
Kotun Daukaka Kara Ta Yi Fatali Da Bukatar Lauyan Abba Kyari

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Sunday Ubua ya shigar inda ya nemi a ba da belinsa.
Ubua dai na hannun damar mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ne, wanda hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta gurfanar dashi gaban kuliya bisa laifin safarar muggan kwayoyi da sauran laifuffuka.
A wani hukunci da aka yanke a ranar Juma’a, kwamitin maibmutane uku na kotun daukaka kara ya ce karar da Ubua ya shigar ba shi da wani dalili kuma ya tabbatar da hukuncin da Mai shari’a Nwite, ya yanke a ranar 28 ga watan Maris din shekarar 2022.
Hukuncin da aka yanke na ranar 28 ga watan Maris ya ki amincewa da bukatar Ubua na neman beli saboda masu gabatar da kara sun gabatar da isassun kayyaki a gaban kotu domin tabbatar da kin amincewa da bukatar neman belin.
Mai shari’a Stephen Adah, a hukuncin da ya yanke, ya bayyana cewa wanda ya shigar da kara bai gabatar da wasu sabbin abubuwa a gaban kotun ba domin bayar da damar kotun ta fice daga matakin farko kan batun da mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yi.
Ubua na fuskantar shari’a tare da Kyari da wasu tsofaffin jami’an hukumar bayar da amsar bayanan sirri, da rundunar bincike da kuma leken asiri ta rundunar ‘yan sandan Najeriya su uku, bisa tuhumar su da laifin safarar miyagun kwayoyi ba bisa ka’ida ba da kuma yunkurin yin magudin hujjoji.