Labarai
Wasu Ma’aikatan INEC Sun Sun Gudanar Da Zanga-zanga Kan Rashin Biyan Su Alawus

Wasu ma’aikatan wucin gadi na Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyan alawus-alawus na sufuri a ranar Asabar.
Hakan ya jawo jinkirin tura kayan zabe da wuri a karamar hukumar Bauchi.
Duk da tattara kayan zaben, ma’aikatan sun ki barin cibiyar tattara sakamakon ta Baba-Sidi.
Amma bayan shiga tsakani da wasu manyan jami’an hukumar ta INEC suka yi, ma’aikatan da suka nuna fushin sun samu albashin bayan sun tashi da karfe 9:15 na safe.