Labarai
Yadda sakamakon zaɓen gwamnan Kano ya kasance

Da sanyin safiyar yau ne hukumar INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamna Farfesa Dikko Ahmad Ibrahim na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC ke rufa masa baya da ƙuri’u 890,705.
Aka kuma ya ƙara da cewa, Sadik Wali, na jam’iyyar PDP shi ne ya zo a matsayin na uku, da ƙuri’u 15,957.
Haka kuma, Sha’aban Ibrahim Sharada na jam’iyyar ADP ya samu ƙuri’u 9,402.