Labarai
Wata Kotu Ta Aike Da Wani Mutum Gidan Yari Bisa Laifin Satar Kaji Biyu

Wata kotu mai daraja ta daya dake yankin Dei-Dei a Abuja ta yankewa wani dan kasuwa mai suna Kingsley Isaac dan shekara 22 hukuncin daurin watanni uku a gidan yari a ranar Litinin, bisa samunsa da laifin satar kaji biyu da kudinsu ya kai N8,000. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Tun da fari rahotanni sun nuna cewa, ‘Yan sanda sun tuhumi Isaac da laifin sata.
Alkalin kotun yankin, Saminu Suleiman, ya baiwa Isaac zabin tarar Naira 10,000 da kuma biyan N45,000 ga wanda ya shigar da karar.
Lauyan mai gabatar da kara, Chinedu Ogada, ya sanar da kotun cewa an yanke hukuncin ne bisa wani laifi da ya faru a ranar 11 ga watan Maris.
Ogada ya ce Abdulaziz Salihu a ranar 11 ga watan Maris ya kai rahoton wurin ‘yan sanda kan lamarin a ofishin ‘yan sanda na Zuba da karfe biyu na safe.
A cewarsa: “Ishak ya je gidan wanda ya kai karar ya kwashe kajinsa guda biyu wadanda aka kiyasta kudinsu ya kai N8,000 ba tare da izininsa ba. Mai laifin ya bude motar mai karar, ya sace kayan motar da kudinsu ya kai N35,000 sannan ya sayar wa wani da ba a sani ba. Amma daga baya aka kama shi aka mika shi ga ‘yan sanda domin gudanar da cikakken bincike.”
Lauyan mai gabatar da kara ya kara da cewa wanda ake tuhumar ya amince da laifin ne a lokacin da ‘yan sanda ke yi masa tambayoyi.
Laifin, in ji shi, ya saba wa tanadin sashe na 287 na kundin laifuffuka na Babban birnin tarayya Abuja.