Labarai
Bola Tinubu ya yi balaguro zuwa ƙasashen ƙetare

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado Bola Tinubu, ya bar gida Najeriya domin zuwa yankin Turai da kuma aikin umara a kasar Saudiyya.
Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yada labarai Mista Tunde Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Larabar makon nan a birnin tarayya Abuja.
Ya ƙara da cewa zaɓaɓɓen shugaban ya bar filin jirgin sama na Murtala Mohammed inda ya nufi nahiyar Turai.
Haka kuma ƙara da cewa, “Zababben shugaban kasan ya yanke shawarar yin hutu ne bayan yaƙin neman zaɓe da lokacin zaɓe domin ya huta a Paris da London.
Ya kuma ce, “Shirye-shiryen zuwa Saudi Arabiya don Umrah da kuma Azumin Ramadan da zai fara ranar Alhamis.