Labarai
Hukumar INEC ya sanar da ranar raba takardun shaidar lashe zaɓe ga gwamnoni da ƴan majalisa

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta saka ranakun bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga sababbin zaɓaɓɓun gwamnoni da ƴan majalisun jihohi.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitinta na yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a Mista Festu Okoye.
Ta cikin sanarwar, INEC ta ce, sashe na 72 (1) na dokar zaɓen Najeriya ta 2022 ne ya ɗora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar samun nasara lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun ƴan takara a cikin kwanaki 14 da yin zaɓe.
Hukumar ta ƙara da cewa, don haka, ta sanya ranar Laraba 29 ga wannan watan da muke ciki na Maris da kuma 31 ga watan dai na Maris a matsayin ranakun bayar da takardun shaidar cin zaɓen.
Haka kuma, Sanarwar ta ce za a bayar da takardar shaidar cin zaɓen ne a harabar ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohi.