Labarai
Hukumar NiMet ta yi hasashen samun ƙwallewar Rana

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin ƙwallewar rana a wasu daga jihohi.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja.
A cewar hukumar mutane za su ji sauyin al’amura na tsawon lokacin da za a kwashe ana fama da zafin ranar.
Haka kuma ta ƙara da cewa jihohin Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da kuma jihar Kwara na daga cikin waɗanda za su fuskanci tsanantar yanayin.
Sauran sun haɗa da Birnin Tarayya Abuja da jihar Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma jihar Borno.
Haka kuma NiMet ta ce, yanayin zafin rana zai ƙaru har zuwa maki 40 a ma’aunin celcius nan da kwanaki biyu masu zuwa.
Haka kuma ta ce, a wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa kuwa zafin ranar zai haura matakin maki 40 a ma’aunin Celcius.