Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida-Gida murnar cin zaɓe

Ɗan takarar gwamnan Kano a zaɓen bana na jamiyyar APC kuma mataimakin gwamna Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya taya sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Engr. Abba Kabir Yusuf murnar lashe zaɓe.
Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana hakan ne ta cikin wani saƙon murya da ya fitar da yammacin yau Laraba.
Haka kuma, ya yi wa abokin karawa tasa addu’a da fatan samun nasara yayin gudanar da mulkinsa.
Gawuna ya kuma ƙara da yi wa kansa da magoya bayan jam’iyyar APC fatan haƙuri da karɓar ƙaddara.