Labarai
Nasarar da Abba Kabir ya samu ta Wucin gadi ce- Ganduje

Gwamnan jihar Kano jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa nasarar da sabon zababben gwamna Engr Abba Kabir Yusif, ya samu ta wucin gadi ce, don kuwa za su daukaka kara kan nasarar tasa a kotu.
Ganduje ya bayyana hakan ne da yammacin yau Asabar bayan kammala addu’ar neman zaman lafiya da ci gaban jihar Kano da aka gudanar a dakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin jihar Kano.
Freedom Radio ta ruwaito cewa a ganawarsa da manema labarai bayan kammala addu’o’in, gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma yi wa shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmad Tunubu, addu’o’in fara mulki cikin nasara a wani bangare na taya shi murnar cika shekaru saba’in da daya da da haihuwa.
Haka kuma ta bayyana cewa Ganduje, ya kuma yi wa Engr Abba Kabir Yusif, addu’a da fatan gudanar da mulki yadda ya dace.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta kafa kwamitin mika mulaki ga sabuwar gwamnati.