Connect with us

Labarai

Zamfara: Ƴan sanda sun duƙufa wajen nemo ɗaliban jami’a mata da ƴan bindiga suka sace

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ta tabbatar da rahoton sace wasu mata biyu ɗaliban jami’ar tarayya ta Gusau da ƴan bindiga suka sace su a daren wayewar yau.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kolo Yusuf psc, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi.

Ta cikin sanarwar, Kwamishinan, ya tabbatar wa al’umma musamman iyalai da kuma mahukuntan jami’ar tarayya ta Gusau cewa, ana ci gaba da kokarin kubutar da daliban jami’ar guda biyu da yan ta’adda suka sace su a safiyar yau Lahadi, inda jami’an tsaro na ‘yan sanda suka tsananta bincike don ceto su.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa, da misalin karfe 1:00 na daren wayewar yau Lahadi 2 ga watan Afrilu ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai farmaki kauyen sabon gida da ke karamar hukumar Bungudu inda suka shiga gidan kwanan ɗalibai mata na jami’ar inda suka kulle wasu mutane biyu da ƙwace wayoyinsu tare da sace ɗalibai matan su biyu da ke karatu a sashen Microbiology na jami’ar.”

” Bayan samun rahoton, tawagar kar ta kwana ta rundunar ‘yan sanda ta isa wurin da lamarin ya faru, sai dai tuni ‘yan bindigar sun  gudu tare da wadanda lamarin ya ritsa da su inda har kawo yanzu ba a gano inda suka buya ba.” a cewar sanarwar

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara tura dakarun da za su ci gaba da aikin ceto wadanda aka yi garkuwa da su, tare da cafke wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet