Labarai
Bauchi: An kashe wani mutum bisa zarginsa da satar Kankana

Wasu mazauna ƙauyen Dallaji da ke yankin ƙaramar hukumar Warji ta jihar Bauchi, sun hallaka wani mutum da ake zargi da satar Kankana ta hanyar yi masa dukan kawo wuƙa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar ta Bauchi, Ahmed Mohammed Wakilin, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Haka kuma ya ƙara da cewa, tuni ƴan sanda suka cafke waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Haka kuma ya ƙara da cewa, binciken farko rundunar ta gudanar ya nuna cewa marigayin mai suna Ibrahim Hashimu, ya kutsa kai cikin wata gona mallakar wani mai suna Mohammed Garba, inda ya ɗauki Kankana guda bakwai da kuɗinsu ya kai Naira 2,000.
Haka kuma, Ya ce, bayan mai gonar ya kama shi ne wasu kuma suka yi masa duka da sanduna wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
Ahmed Muhammad Wakil, ya ƙara da cewa, kwamishinan ƴan sandan jihar Aminu Alhassan ya bayyana rashin jin daɗi bisa matakin da mutanen suka ɗauka, yana mai cewa kamata ya yi idan an samu wanda ake zargi da laifi a riƙa miƙa shi ga hukuma.