Ilimi
Gwamnatin El-rufa’i ta mayar da Malaman makaranta da ta kora a baya

Gwamnatin jihar Kaduna, ta amince da mayar da malaman makarantun firamare fiye da duɓu ɗaya da ta sallama a Yunin 2022 bayan yi musu wata jarrabawar tabbatar da ƙwarewarsu.
Jami’ar hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Hajiya Hauwa Muhammad ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Larabar makon nan.
Hajiya Hauwa ta ce, malamai 1,266 ne aka yi wa jarrabawar gwajin cancantar yayin da 22 a cikinsu aka tsame su daga jadawalin albashin gwamnati.
Tun a watan Yunin bara ne ma’aikatar ilimin ta kori malaman Firamare 2,357 saboda gaza tsallake jarrabawar.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa an sallami malamai 2,192 saboda ƙin rubuta jarabawar yayin da malamai 165 kuma aka kore su saboda rashin tabuka abin a zo a gani.