Labarai
Zan koma Daura idan na ƙarasa mulki- Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce, zai koma mahaifarsa Daura idan ya damƙa mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Mista Femi Adesina ya fitar.
Sanarwar ta ruwaito cewa, shugaba Muhammadu Buhari, ya furta hakan ne a Larabar makon nan yayin da ya karɓi baƙuncin Jakadiyar Birtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing.
Haka kuma ta cikin sanarwar, shugaba Buhari ya yaba wa Birtaniya bisa tallafa wa Najeriya a ɓangarori da dama musamman sake gina yankin Arewa maso Gabas.
Shugaba Buhari, ya ƙara da cewa, Birtaniya ta kasance gida ga ƴan Najeriya da dama, tare da cewa dangataƙar ƙasashen biyu za ta ci gaba da wanzuwa.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Ita kuwa Jakadiyar mai barin gado cewa ta yi, Ba ta ji daɗin barin Najeriya ba musamman ma ganin cewa ta ga abubuwa da dama a ƙasar kama daga al’adu da raye-raye da kuma wakokin ƴan ƙasar masu daɗi.