Labarai
Hukumar Kwastam Ta Yi Gargadi Game Da Shafin Daukar Ma’aikata Na Bogi

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar daukar ma’aikata da ke yawo a yanar gizo.
Jami’in hulda da jama’a na NCS, babban Sufeton Kwastam, Abdullahi Maiwada ne ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Abuja ranar Juma’a.
Maiwada ya bayyana sanarwar a matsayin ta bogi, yana mai cewa hukumar NCS ba ta daukar ma’aikata a halin yanzu.
“Sanarwar aiki ne na rashin gaskiya da kuma yunkurin damfarar ‘yan Najeriya.
“Sanarwar daukar ma’aikata tare ta hanyar yanar gizon https://recruitmentfile.net/nigeria-customs-recruitment/ karya ce kuma ya kamata a yi watsi da ita.
“Akwai bayanai da yawa da ke nuna cewa sanarwar ba ta fito daga Hukumar Kwastam ba, musamman yankin.
“Shafin yanar gizon mu shine www.customs.gov.ng. Ba ma amfani da .net, don haka gaba ɗaya karya ne.
“A halin yanzu kwastan ba ta daukar ma’aikata kuma idan zata yi hakan, zai kasance a shafin yanar gizon hukumar kawai,” in ji shi.
Kakakin ya ce ya kamata wadanda ke da hannu a irin wannan aika-aika su daina, ya kara da cewa sharri ne. (NAN)
Abubakar isah
08/06/2023 at 11:27 am
Allah ya jikan shi