Tsaro
Wasu ‘Yan Ta’adda Sun Sace Akalla Mutane 60 A Zamfara, Da Katsina

Rahotanni sun ce ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane 60 a jihohin Zamfara da Katsina.
Wadanda aka sacen wadanda aka ce yawancinsu yara ne ‘yan kabilar Kucheri, Wanzamai, da Danwuro a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, da kuma garin Yankara dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Karamar hukumar Faskari a Katsina da kuma karamar hukumar Tsafe a Zamfara garuruwan suna kan iyaka ne.
An ce an yi garkuwa da mutanen ne a safiyar ranar Juma’a a lokacin da ‘yan ta’addan ke tafiya daga dajin Sububu a Zamfara zuwa wani dajin da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Majiyar wadda ta zanta da BBC Hausa a madadin sauran mazauna wurin ta ce mutum daya ya samu munanan raunuka kuma ana yi masa jinya.
Wani mazaunin karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara Ahmad Kucheri, ya ce ‘yan ta’addan sun samu raunuka daga sojoji kuma suna gudun hijira daga jihar, inda ya kara da cewa ‘yan bindigar sun fara garkuwa da mutanen da suka gani a hanyarsu ta ficewa daga jihar.
Ya ce yawancin wadanda abin ya shafa an sace su ne daga gonakinsu, yayin da wasu kuma yara ne da suka je diban itace a daji.
“’Yan bindigar na tafiya ne daga dajin Sububu zuwa bangaren Birnin-Gwari. Don haka sai suka ga mutane a cikin daji suna dibar itace, suka debo, wasu yara suna diban takin gida, wasu suna aikin hakar ma’adinai, sai suka tara su gaba daya suka koma bangaren Birnin-Gwari zuwa Jihar Neja,” inji Channels Television. An nakalto Kucheri yana cewa.
“Ba su harbe kowa ko kashe kowa ba, kawai sun tara mutane ba yara kawai ba amma duk wanda suka gani a hanya.”
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Da aka tuntuba domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Zamfara, Mohammed Shehu, bai kai ga amsa kira ko sakon da aka aike masa ba.