Labarai
Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da kashe-kashen Benue

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi Alla-wadai bisa kashe-kashen a aka yi a baya-bayan nan a jihar Benue.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarawa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar.
Ta cikin sanarwar, Shugaba Buhari ya ce za a yi duk mai yiyuwa wajen kawo ƙarhen irin waɗannan tashe-tashen hankula ba ma a jihar ba kaɗai, a duk faɗin Najeriya.
Haka kuma, Ya bayar da umarnin zaƙulo maharan da suka hallaka mutane a jihar ta Benue domin a tabbatar sun fuskanci hukunci bisa laifin.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙara da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, tare da umartar jami’an tsaro da su tabbatar da cewa sun zaƙulo waɗanda suka aikata ta’asar.
A makon da muka yi ban-kwana da shi ne wasu ɓata gare suka kashe mutane da dama a ƙauyen Umogidi da ke yankin ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar.