Labarai
EFCC Ta Kama Wasu Mutane 11 Bisa Zargim Su Da Damfarar Yanar Gizo A Borno

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kama wasu mutane 11 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a kananan hukumomin Jere da Maiduguri a jihar Borno.
Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Ya ce wadanda ake zargin da aka kama a ranar Laraba sun hada da Olatunji Sherif, Bright Felix, Jude Magaji, Jonah Jondi, Ojobaro Abdullahi, Jerry Zizighi da Micah Joseph.
Sauran sun hada da: Mari Ayuba, Ibrahim Abdullahi, Adam Abiodun da Victor Chinonso Okolieaboh.
Uwujaren ya ce an kama su ne a wani samame da aka kai bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan da ake zarginsu da aikatawa.
“Kayan da aka kwato a gidansu sun hada da Mercedes Benz GLK 350 guda daya, mota kirar Toyota Corolla saloon, wayoyin hannu, MTN 4G Wi-Fi da kuma injin cajin waya.
“Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike,” in ji shi. (NAN)