Labarai
Rundunar ƴan sanda za ta baza jami’ai fiye da 2,000 don kula da zaɓen Kano

Rundunar ƴan sandan Najeriya, ta bayyana cewa, za ta baza jami’ai fiye da dubu biyu yayin gudanar da zaɓen da bai kammala ba a wasu ƙananan hukumomin Kano a gobe Asabar.
Babban sufeton ƴan sandan Usman Alkali Baba, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai yau Juma’a.
Usman Alkali Baba wanda ya samu wakilcin mataimakinsa AIG Ibrahim Sani Kaoje, ya kuma gargaɗi ƴan siyasa da magoya bayansu da kuma masu shirin tayar da hankalin al’umma a wajen kaɗa ƙuri’a da su guji yin hakan ko kuma su haɗu da fushin rundunar.
Haka kuma ya buƙaci al’umma da su bai wa rundunar ƴan sandan haɗin kai wajen ganin ta samu nasara a aikin da za ta gudanar yayin zaɓen.