Labarai
Alhassan Ado Doguwa ya sake lashe zaɓe

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa, ya sake lashe zaɓen kujerar majalisar tarayya ta ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada a Jihar Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, Tun a shekarar 2007 Alhassan Ado ya shiga zauren majalisar.
A yanzu ya zama cewa Doguwa, ya lashe zaɓen kujerar karo na biyar a matsayin mai wakiltar kananan hukumomin.