Labarai
Ahmadu Fintiri ya sake lashe zaɓen gwamnan Adamawa

Hukumar zaɓe INEC, ta sanar da sunan gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa.
BBC ta ruwaito cewa, jami’in sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Farfesa Mohammed Mele, ne ya bayyana sakamakon da yammacin yau Talata.
Farfesa Mele, ya ce, gwamna Fintiri, ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 430,861, yayin da abokiyar karawarsa Aisha Ɗahiru Binani ta samu ƙuri’u 398,788.
Yanzu haka dai gwamna Ahmadu Fintiri ya samu damar shugabancin jihar ta Adamawa a karo na biyu.