Connect with us

Labarai

Da Dumi-Duminsa: Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Direban Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Daniel Ogoshi, direban mataimakin gwamnan Nasarawa Dr Emmanuel Akabe.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an dauke Ogoshi ne daga gidan abokinsa da misalin karfe 9:30 na dare a Ombi 2, da ke College of Agric, Kwandere road Lafia, inda ya bar wayarsa da motarsa.

Wani abokin ’yan uwa da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kira shi da misalin karfe 9 na dare wasu masu garkuwa da mutane sun tafi da dan uwansa.

Nan take abokin dangin ya sanar da ’yan sandan da suka garzaya wurin amma tuni masu garkuwa da mutanen suka gudu da wanda lamarin ya shafa.

Jami’in yada labarai na mataimakin gwamnan, Emmanuel Eyima, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sanar da shi halin da ake ciki amma bai da cikakken bayani kan abin da ya faru.

Shi ma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce ‘yan sanda na kan bincike.

Sai dai ya bayyana cewa ba zai kara yin tsokaci kan lamarin ba har sai an tabbatar da ingancinsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet