Labarai
INEC za ta bai wa Fintiri Shaidar cin zaɓe yau Laraba

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC, ta bayyana cewa za ta bai wa gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da mataimakiyarsa farfesa Kaletapwa Farauta shaidar lashe zaɓe a karo na biyu.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafi ta na Twitter.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, a dai yau ɗin za ta bai wa sauran sababbin ƴan majalisar tarayya da na jihohi shaidar cin zaɓensu
BBC ta ruwaito cewa, a jiya Talata ne jami’in sanar da sakamakon zaɓen jihar Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya bayyana Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓe da ƙuri’u 430,861.