Labarai
Sarkin Musulmi ya bayyana Juma’a a matsayin ranar Sallah

Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Najeriya Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal.
Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa yana mai cewa, ganin jinjirin watan da aka yi a wasu sassan Najeriya ne ya sanya ayyana gobe Juma’a a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal na shekarar 1444.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa, Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaidu da ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan na bana.
Ta cikin sanarwar dai, Sarkin Musulmi, kuma umarci musulmin Najeriya da su ajiye azumi domin an ga wata, su kuma yi shirin zuwa masallaci domin halartar Sallar Idi.