Connect with us

Labarai

Lafiya ta Garau- Tinubu ga Ƴan Najeriya

Sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar da cewa, yana cikin koshin lafiya, kuma a shirye yaki ya jagoranci kasar nan yadda ya kamata.

Hakan ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewar zababben shugaban bashi da cikakkiyar lafiya, dalilin kenan da ya sanya shi zuwa wasu kasashen duniya bayan bayyana sakamakon zaben da aka gudanar.

Hakan na ɗauke ne cikin wata sanarwar da hadimin shugaban Tunde Rahman ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce, Bola Tinubu, ya je ƙasashen Faransa da London da kuma Saudi Arebia inda ya gudanar da aikin Umrah, domin ya huta bayan kammala hidimar zabe.

A don haka sanarwar ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewar Bola Tinubu bashi da lafiya, wadda labarin bashi da tushe ballantana makama.

Da yammacin jiya Litinin ne sabon zaɓaɓɓen shugaban ya dawo gida Najeriya tare da mai dakinsa Oluremi Tinubu, inda suka samu tarba daga magoya bayansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet