Connect with us

Labarai

Ƴan bindiga sun sace mutane a yankin Abuja

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu mutane 29 da suka haɗa da manya maza, matan aure da yara a ƙauyen Yewuti, mahaifar tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwali, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti.

Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa, wasu matan aure biyu, Zainab Umar da Aisha Zubairu, sun tsere daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su a lokacin da aka kai su cikin daji.

Daga cikin waɗanda aka sace akwai Idris Mohammed, Abdullahi Zubairu, Sani S. Magani, Peter Modu, Ibrahim Mamman, Yellow Abdulrasheed, Musa Suleiman, Simbiya Ishaku, Sumaiya Ibrahim, Muktari Yunusa da Mohammed Yeluwa da Rahmat Shagari.

Sauran waɗanda abin ya shafa sun haxa da, Sumaiya Abubakar Yelwa, Mohammed Yelwa, Maimuna Muhammad, Hussaini Ya Nda Agyana, Hamza Ibrahim, Lantana Yunusa, Nabila Agyana, Rufai Salihu, Nafisa Aminu, Kasimu Adamu, Abako Adamu, Abdulyakin Aliyu, Lukman Aliyu, Rahina Audu, Abdulrazak Usman, Sadiya Usman, Darius Samuel da Japheth Osu.

Haka kuma ta bayyana cewa, wani mazaunin garin Yewuti, wanda ya tsere, Shuaibu Ndako, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Talata, inda masu garkuwa da mutane da yawa suka mamaye al’ummar.

Ya ce masu garkuwa da mutanen da suka raba kan su rukuni-rukuni, sun je gidaje takwas ne a yayin da suke ta harbe-harbe, inda suka tafi da mazauna yankin ciki har da yara da matan aure cikin daji.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet