Connect with us

Labarai

Ƴan Boko Haram 135 sun miƙa wuya bayan da sojoji suka kashe wasu su 35

Rahotonni daga jihar Borno na nuni da cewa, dakarun soja sun kashe ƴan ta’addar Boko Haram su 35, yayin da wasu kuma su 135 tare da iyalansu suka miƙa wuya ga sojojin a ƙaramar hukumar Bama ta Jihar Borno.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, miƙa wuyan ƴan ta’addar ya biyo bayan ƙarin farmakin da sojojin rundunar Operation Hadin Kai suke kai wa ƴan tada ƙayar bayan a Dajin Sambisa.

Haka kuma ta bayyana cewa, “Akwai ƙarin ƴan ta’adda 113 daga garuruwan Balangaje da Bula-Waziri da Bula – Kurma da Sabil – Huda waɗanda suka miƙa wuya ga sojoji a Yamteke,”

Haka kuma jaridar ta ƙara da cewa, ƴan ta’addan sun ajiye makamansu ne mako guda bayan sojoji da mayaƙan sa kai na Civilian Joint Task Force sun tsananata kai farmaki a maboyarsu.

Haka kuma ta ce, wasu ƙarin ƴan ta’addan tare da iyalansu da suka haɗa da ƙananan yara 13 da mata daga kauyukan Nguru Soye da Kelani sun mika wuya ga sojojin Bataliya ta 202 da ke Bama.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet