Labarai
CBN ya musanta batun janye sababbin kuɗi

Babban Bankin Najeriya CBN, ya musanta batun cewa, yana ƙoƙarin yanke shawarar janye sabbin takardun kuɗi na Naira 200 da 500 da kuma Naira 1,000.
Babban bankin ya musanta hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin Draktan yaɗa labarunsa Abdulmumin Isa.
Ta cikin sanarwar dai, CBN ɗin, ya bayyana batun janye sababbin kuɗin a matsayin labari maras tushe bare makama.
Haka kuma CBN ya ƙara da cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin kuɗin kamar yadda ake yi a halin yanzu.