Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ake Zargin Ya Hallaka Mahaifiyarsa A Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke Ibrahim Musa mai shekaru 22, wanda ake zargi da dabawa mahaifiyarsa mai shekaru 50 wuka a unguwar Rimin Kebe dake karamar hukumar Ungogo, jihar Kano.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an kama wanda ake zargin ne a wata maboyar miyagun da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a Kano.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa sannan kuma ya amsa laifin yin mu’amala da miyagun kwayoyi.
Ya bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala cikakken bincike.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, ya yaba wa wadanda suka taimaka da bayanan da suka kai ga kama shi.