Labarai
Kidayar 2023 Za Ta Magance Matsalolin Da Suka Addabi Kasar — NPC

Kwamishinan hukumar kidaya ta Kasa, Dr Abdulmalik Durunguwa, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kidayar 2023 za ta magance dimbin matsalolin da suka addabi kasar nan.
Durunguwa mai wakiltar jihar Kaduna a hukumar ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan kungiyar ‘yan jaridu ta kudancin Kaduna a Abuja ranar Juma’a.
Ya ce galibin al’amuran da suka shafi kasar nan za su kare ne idan an gudanar da kidayar jama’a yadda ya dace, inda ya ce aikin zai nuna wa gwamnati inda matsalolin suke.
A cewarsa, kidayar za ta samar da bayanan da ake bukata ga gwamnati da abokan huldar ta don tsara yadda za a biya bukatun jama’a da yadda za a dora kasar nan kan turbar ci gaba mai dorewa.
“Bayanan da ake buƙata sun fi alaka da inda kuke zaune ba ƙauyenku ko jiharku ba saboda ainihin bayanan shine magance matsalolin mutane a duk inda suke.
“Kasar na bukatar sanin abubuwan da suka hada da yanayin al’ummarta don haka ya kamata a kirga mutane a duk inda suke.”
Ya kuma yi kira ga duk wani dan Najeriya da ya tsaya a inda za a kirga su domin gwamnati ta san jama’a don su taimaka wa gwamnati wajen yin shiri.
A cewarsa, bayan kidayar jama’a, gwamnati za ta samu takardar aiki da za a yi amfani da ita wajen magance kalubale, musamman da suka shafi mutanen da ke zaune a sassan kasar.