Connect with us

Labarai

APC Ta Bayyana Wadanda Za Su Shugabanci Majalisu Na 10

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa, ya fitar da jadawalin yadda shugabancin majalisun kasa zasu kasance, ta hanyar amfani da shiyya shiyya domin tabbatar da adalci ga kowane bangare na kasar nan. Kamar yadda CHANNELS TV ta ruwaito.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Felix Morka sakataren wayar da kai na kasa karkashin kwamitin, wadda aka rabawa manema labarai da yammacin Litinin din nan ta ce:

Shugaban majalisar dattawa, zai fito daga yankin kudu maso Kudu, inda suka zabi Samata Godswill Akpabio, sai kuma mataimakinsa daga yankin Arewa Maso Yamma inda aka ɗauki Sanata Barau Jibril daga jihar Kano.

Sauran shugabancin majalisar sune Abbas Tajudden daga jihar Kaduna a matsayin shugaban majalisar wakilai, sai kuma Ben Kalu daga jihar Abia a matsayin mataimakinsa.

Morka yace sanar da zaben shiyyoyin ya biyo bayan wani zaman gaggawa da suka gudanar, bisa kulawar sabon zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki.

Daga nan sai jam’iyyar ta bukaci daukacin shugabanni al’umma da kowa kan ci gaba da aiki yadda ya kamata da kuma addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa a kasa baki daya.

A wani labarin kuma: Da Yuwuwar Yan wasan Barcelona Biyu, Su bi Messi Zuwa Sabuwar Kungiyarsa

Al-Hilal na fatan zawarcin Lionel Messi daga Paris Saint-Germain a wannan bazarar, ta hanyar kulla yarjejeniya da takwarorinsa na Barcelona Sergio Busquets da Jordi Alba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

An yi imanin cewa kungiyar ta dake buga gasar Saudi Pro League ta gabatar da kudin da ya kai fam miliyan 400 ga Messi, wanda ke shirin zama wakili na kyauta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet