Labarai
Kungiyar Al’Hilal ta bai wa Messi Pam miliyan 260 don ya buga mata kwallo

Kungiyar Kwallon Kafa ta Al Hilal da ke Saudiya ta yi wa Lionel Messi na PSG tayin zunzurutun Pam miliyan 260 a matsayin albashinsa na shekara guda da za ran ya koma kungiyar da taka leda.
Akwai yiwuwar Messi ya ci gaba da zama a PSG har zuwa karshen wannan kaka kafin ya yanke shawara game da makomarsa.
Kimanin wata guda kenan da aka yi wa Messi wannan gwaggwabar tayin amma bai yi gaggawar amincewa da ita ba.
A maimakon haka, dan wasan na Argentina ya ci gaba da mayar da hankalinsa kan wasannin PSG a wannan kaka duk kuwa da dakatarwar da kungiyar ta yi masa ta tsawon makwanni biyu.
Dan wasan na fatan kammala wannan kaka da kofin gasar Lig ta Faransa a hannunsa
Wasu rahotanni a Spain sun ce, dan wasan mai shekaru 35 zai raba gari da PSG a karshen wannan kaka kuma ana sa ran zai ki amince wa komawa Barcelona tare da tafiya zuwa yankin gabas ta tsakiya.
Babu mamaki Messi din zai bi sahun tsohon abokin hamayyarsa a duniyar tamola, Cristiano Ronaldo wanda ya koma Saudiya da taka leda.