Majalisar Tarayya, ta fara yin shirin fara horas da sababbin ƴan majalisar dattawan kan sa in makamar ayyukanta gabanin rantsar da su.
BBC ta ruwaito cewa, bitar za ta taimaka wajen ilimantar da sababbin ƴan majalisar wajen sanin makamar aikin da za su gudanar a zauren.
Haka kuma ta ƙara da cewa, cibiyar kula da ayyukan majalisa da dimokradiyya a ƙasar ta ce bitar na da matuƙar muhimmanci kasancewar fiye da kashi 70 cikin 100, na zaɓaɓɓun ‘yan majalisar, karon su na farko kenan da suke zuwa majalisar.
