Labarai
Ƴan sanda sun cafke jami’an tsaro da ke yin Fashi

Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta ce, ta cafke wani jami’an sojan ruwa Ibrahim Adamu, mai shekara 25 da wani jami’in gidan ajiya da gyaran hali Abdullahi Abdulwahab, mai shekara 26, bisa zargin su da yin Fashi da Makami.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ana zargin jami’an biyu ne da aikata laifin fashi da makami tare da ƙwacen mota.
Haka kuma ta ce, mai magana da yawun rundunar SP Chidi Nwabuzor, yayin taso ƙeyar waɗanda ake zargin ranar Talatar makon nan, ya bayyana cewa jami’an su ne suka cafke su ne sanye da kayan sojoji a Ekpoma, biyo bayan samun bayanan sirri.
Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun farmaki direban motar ƙirar C300 Mercedes Benz wacce ba ta da rajista a Sapele, cikin jihar Delta, suka ƙwace motar daga hannun sa sannan suka tilasta masa tura mu su N400,000 a cikin asusun bankin su.
Haka kuma ya ce, waɗanda ake zargin suna shirin tafiya da motar ne birnin tarayya Abuja, lokacin da ƴan sanda suka cafke su a Ekpoma, cikin jihar Edo.
Ya ce, “Waɗanda ake zargin sun bayar da bayanai inda suka yi iƙirarin cewa su jami’an sojin ruwa ne da gandiroba.”
Nwabuzor ya ƙara da cewa, an kwato motar da kayan sojojin da su ke a hannun waɗanda ake zargin. Da ya ke magana da manema labarai, Ibrahim Adamu, wanda ya shiga aikin soja a shekarar 2019, ya ce an cafke shi ne bisa satar mota ƙirar Mercedes Benz C300 a jihar Delta.