Labarai
An dawo da ƙarin Ƴan Najeriya 125 daga Sudan

Gwamnatin tarayya, ta sake kawo ƙarin ƴan Najeriya 125 daga ƙasar Sudan mai fama da rikici.
BBC ta ruwaito cewa, Jirgin Tarco B737-300 ne ya kwaso mutanen daga Port Sudan inda kuma ya sauke su a filin jirgin sama na birnin tarayya Abuja da tsakar ranar yau Asabar.
Haka kuma, ta ruwaito cewa, zuwa yanzu adadin waɗanda aka dawo da su ɗin sun zama kimanin mutane 2,371.
A ranar uku ga watan Mayu ne jirgin farko ɗauke da ‘yan ƙasar daga Sudan ya sauka a filin jirgin Abuja.