Connect with us

Labarai

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aikin Gargadi A Nigeria

Kungiyar Likitoci masu Neman kwarewa ta Najeriya ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.

Fara yajin aikin ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun kungiyar tsawon lokaci.

Likitocin sun ce za a fara yajin aikin ne da karfe 8 na safe ranar Laraba 17 ga watan Mayu, kuma za a kammala yajin aikin ne a ranar Litinin 22 ga watan Mayu da karfe 8 na safe.

Wannan shi ne shawarar da suka cimma bayan taron majalisar zartarwa ta kasa na tsawon sa’o’i shida da rabi wanda aka yi ranar Litinin.

A ranar 29 ga Afrilu, 2023, NARD ta ba da wa’adin makonni biyu ga Gwamnatin Tarayya don biyan bukatunta ko kuma ta fuskanci rashin jituwa daga bangaren su.

Wa’adin ya ƙare a ranar Asabar, Mayu 13, 2023.

Likitocin dai na neman a kara musu tsarin albashin su zuwa kashi 200 cikin 100 na yawan albashin da likitocin ke karba a halin yanzu.

Likitocin sun kuma bukaci a gaggauta janye kudirin dokar tilasta wa wadanda suka kammala karatun likitanci da na hakori yin aikin tilas na tsawon shekaru biyar a Najeriya kafin a ba su cikakken lasisin yin aikin da sauran wasu bukatu nasu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet