Labarai
Tsagin Ganduje ya bai wa kwamitin Kwankwasiyya rahoton miƙa mulki

Tsagin gwamnan Kano mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da rahoton mika mulki ga kwamitin sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran sabon zaɓaɓɓen gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da yammacin yau Laraba.
Sanarwar ta ce, a wata ganawa da aka yi a gidan gwamnatin Kano, gwamna Ganduje wanda sakataren gwamnatinsa Alhaji Usman Alhaji, ya wakilci shi, ya bayyana ƙudirinsa na miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun bana.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Ganduje ya bukaci gwamnati mai jiran gado da ta yi nazari kan rahoton mika mulkin tare da bayar da ra’ayin sa.
“A nasa jawabin, zababben gwamnan jihar Kano H.E.Abba Kabir Yusuf, wanda shugaban kwamitin mika mulki Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya wakilta ya nuna cewa kwamitinsa zai kai rahoto ga gwamna mai jiran gado tare da nazari kan sa” a cewar Sanarwar.
Sanarwar ta ce za a bai wa jama’a cikakkun bayanai game da bikin kaddamarwa bayan an cimma wasu yarjejeniyoyi tsakanin gwamnatoci masu barin gado da masu jiran gado.