Labarai
Ana bin Kano bashin sama da Naira biliyan 240- Gwamna Abba Kabir

Sabon gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa, ya karɓi kundin mulkin jihar mai ɗauke da bashin fiye da Naira biliyan 240.
Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne a yau Litinin.
Haka kuma, ya sha alwashin binciko yadda aka yi gwamnatin da ya gada ta tsohon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta ciyo bashin da kuma yadda aka tafiyar da shi.