Labarai
Tinubu ya sha rantsuwar kama aiki

Sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Sanata Bola Ahmad Tinubu, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasa.
An rantsar da sabon shugaban ne da safiyar yau Litinin 29 ga watan Mayu kamar yadda yake bisa ƙa’ida a Najeriya
Tinubu dai shi ne shugaban ƙasa na 16 a jerin shugabannin Najeriya.
Bayan shan rantsuwar, sabon shugaban, ya kuma sanya hannu a takardar rantsuwar kama aiki nan take.