Labarai
Tinubu ya gana da Emiefele a Aso Villa

Gwamnan CBN Mista Godwin Emefiele, ya da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, sun gana a fadar mulkin Najeriya ta Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.
Rahotonni sun bayyana cewa, Shugaba Tinubu, ya shiga fadar ne misalin ƙarfe 2:30 na ranar yau Talata.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, shugaban ya samu tarba daga mataimakinsa Kashim Shettima da gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele da shugaban kamfanin Mai NNPC Mele Kyari da Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da kuma babban sakataren ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Tijjani Umar da wasu sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya.