Labarai
Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane Biyu Da Ake Zarginsu Da Alert Na Bogi A Kano

Rundunar ‘yan Sanda shiyya ta daya (Zone 1) ta kama wasj magidanta guda biyu da ake zarginsu da yin sakon kudi na bogi wato Alerts inda suka yi siyayya a katafarun shagunan al’umma.
Kakakin rundunar shiyya ta 1 SP Abubakar Rayyanu Anbursa shi ne ya bayyana haka da yammacin ranar Juma’a a wata ganawarsa da manema labarai.
SP Abubakar Anbursa ya ce sun kamo mutanen ne bayan samun Korafe-korafe daga wasu masu katafaran kantin sayar da kayan gine-gine na miliyoyin Naira tun a shekarar bara ta 2022.
Kakakin shiyya 1 ya ce magidantan sun hada da Alkasim Muhammad Bauni da Dahiru Muhammad Gwaska, sun kamo su ne a wurare daban-daban.