Labarai
Kano: Ƴan sanda sun cafke matasa 49 da ake zargi da ɗibar kaya a Triumph

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce, ta fara bincike kan matasa 49 da ta kama su bisa zargin satar kayan gini a shagunan Triumph ta ƙaramar hukumar Fagge.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce, rundunar ta kama matasan ne da kayayyakin sata da suka hada da na’urar sanyaya ɗaki guda huɗu Ƙofofi da Tagogi da sauran wasu kayayyaki.
Haka kuma sanarwar ta ce, kwamishinan ƴan sandan Kano Muhammad Hussain Gumel ya bada umarnin ci gaba da binciken matasan domin gurfanar da su a gaban Kotu.
Kiyawa ta cikin sanarwar ya kuma ce, Kwamishinan ƴan sandan na Kano, ya kuma yi kira ga iyayen yara da kuma masu fada a ji a unguwanni da su riƙa gargaɗar matasa da su ƙaurace wa satar kayan mutane, don kuwa rundunar ba za ta saurara wa irin waɗannan matasa ba.