Labarai
Rusau: Gwamnatin Kano Ta Kalubalanci Masu Ganin Baikenta

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya jaddada aniyar gwamnati na ci gaba da rushe haramtattun gine-gine.
Rusa wadannan haramtattun gine-gine anyi shine domin tabbatar da ci gaban birane da kuma kare muradun jama’a.
“Me ya sa mutanen da ke adawa da rugujewar suka yi shiru, musamman malaman addini, a lokacin da tsohon gwamnan yake sayar da kadarorin gwamnati.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jaddada aniyar gwamnati na ci gaba da rusa gine-ginen da aka yi su ba bisa ka’ida ba, wanda gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Ganduje ta fara.
Da yake jawabi a wata ganawa da mambobin kungiyar Progressive Tarauni a gidan gwamnati a daren ranar Alhamis, mataimakin gwamnan ya jaddada muhimmancin bin doka da oda a cikin birane.
Abdussalam ya jaddada wajabcin rusa wadannan gine-gine domin tabbatar da ci gaban birane da kuma kare muradun jama’a.
Ya bayyana damuwarsa game da mummunan tasirin da ba a kayyade ba a kan ababen more rayuwa, da magudanan ruwa, da lafiyar jama’a.
“Ku yi tunanin yadda gwamnatin da ta shude ta sayar da kadarorin al’umma don amfanin kan su, ba tare da la’akari da illar da ke tattare da al’umma ba.
“Rabawa da sayar da filaye a Massalacin Waje mai dimbin tarihi da ke karamar hukumar Fagge da kuma wasu sassa na filin Sallar Idi, wadanda dukkansu suna da mahimmiyar al’adu da addini,” in ji mataimakin gwamnan.
“Me ya sa mutanen da ke adawa da rugujewar suka yi shiru, musamman malaman addini, a lokacin da tsohon gwamnan yake sayar da kadarorin gwamnati ga iyalansa da makusantansa? Ya kara da cewa.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake sayar da wasu sassa na makabartu domin gina shaguna, yayin da ya jaddada kokarin da gwamnati mai ci ke yi na inganta irin wadannan wuraren.