Connect with us

Labarai

EFCC Ta Gurfanar Da Jami’an Kula Da Asusun Gwamnatin Katsina A Kotu

 

Hukumar Yaki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa ta’annati (EFCC) a ranar Alhamis din da ta gabata ta gurfanar da wasu jami’an kula da asusun gwamnatin jihar Katsina biyu a gaban kuliya, bisa samun su da laifin damfarar kusan Naira miliyan 289.

Wadanda ake zargin Sa’adu Maiwada da Sani Lawal sun aikata laifukan ne a matsayinsu na ma’ajin kudi da kuma mataimakin ma’aji a ofishin Akanta-Janar na Jihar Katsina.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar, ya ce an gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban babbar kotun jihar Katsina bisa laifuka biyar da suka hada da hada baki da kuma cin amana.

Wadanda ake tuhumar sun hada baki ne tare da canza Naira miliyan 289 domin amfanin kansu a shekarar 2017.

An gurfanar da wani mataimakin Akanta Janar na Katsina, da laifin zamba N289m A yau ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Sa’adu Maiwada da Sani Lawal BK a gaban mai shari’a Musa Danladi na babbar kotun jihar Katsina bisa tuhumar su da laifuka biyar da suka hada da hada baki da kuma zamba.

Wadanda ake tuhumar dai a matsayinsu na ma’ajin kudi na wancan lokacin da kuma mataimakin babban ma’ajin na ofishin Akanta Janar na jihar Katsina, sun yi zargin hada baki da kuma karkatar da kudaden da suka kai naira miliyan 289,000,000 (Naira miliyan dari biyu da tamanin da tara) daga asusun jihar Katsina.

Bincike ya nuna cewa wadanda ake tuhumar sun wawure kudaden ta asusun kamfanin Integrated Gas Services Limited, kamfanin da wanda ake kara na farko (Maiwada) Darakta ne.

An kuma yi zargin an karkatar da kudi N49,000,000 daga asusun Integrated Gas Services Limited zuwa asusun mai kara na biyu (Lawal BK) wanda yanzu shi ne Mataimakin Akanta Janar na jihar.

Lauyan wadanda ake kara, J B Isra’ila ya gabatar da bukatar belin ta baki a madadin wadanda ya ke karewa amma masu gabatar da kara sun ki amincewa da bukatar.

Mai shari’a Danladi, ya amince da bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi naira miliyan biyar (N5,000,000) kowanne.

Kotun ta umarci kowane wanda ake tuhuma ya bayar da wanda zai tsaya masa dake da kadarori a Katsina tare da gabatar da wasikun gabatarwa daga wani basaraken gargajiya.

An dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga Yuli, 2023 don shari’a.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet