Siyasa
Jibril Isma’il Falgore ya zama sabon shugaban majalisar Kano

Mambobin majalisar dokokin jihar Kano, sun zaɓi wakilin Karamar Hukumar Rogo, Jibril Ismail Falgore a matsayin sabon shugaban majalisar.
Ƴan majalisar sun zaɓe shi ne da safiyar yau Talata, bayan da mai riƙon Akawun majalisar ya rantsar da mambobin.
Haka kuma, wakilan, sun zaɓi wakilin ƙananan Rimin Gado da Tofa Muhammad Bello Butu-Butu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.