Labarai
Abba Gida-gida ya mayar da Muhyi shugabancin PCACC

Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, muƙaminsa na shugabancin Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi ta cin hanci ta jihar.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce gwamnan ya mayar da shi ne nan take bisa biyayya ga umarnin kotu.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Tsohuwar gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ce ta dakatar da Muhuyi Magaji daga kujerarsa.
Sai dai ya garzaya kotu bisa da’awar cewa an dakatar da shi ba bisa ƙa’ida ba.
A watan Yunin nan ne kuma kotun ta tabbatar da shi a muƙamin nasa.