Labarai
Za mu sake gina Shatale-talen da muka rushe- Gwamnatin Abba Gida-gida

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Engr. Abba Kabir Yusuf, ta ce, za ta sake gina Shatale-talen kofar gidan gwamnati da ta rushe a kusa da gadar sama ta Na’ibawa.
Muƙaddashin Sakataren yaɗa Labaran gwamnan jihar Malam Hisham Habib, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar a daren jiya Lahadi.
Sanarwar ta ce, Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, ya gana da Kaltume Ana wadda ta yi zanen shatale-talen mai dauke da alamar cikar jihar Kano shekaru 50 da kafuwa.
Haka kuma ta ƙara da cewa gwamnatin ta cimma matsayar sake gina sabon shataletalen mai inganci domin kara kawata jihar Kano.
A baya dai, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ne ya bada umarnin rushe shatae-talen saboda dalilan tsaro tare da kudirta sake gina shi a wajen da ya dace a cewar sanarwar.