Featured
Matuƙar ƴan Najeriya ba suyi fito na fito da shugabanni ba, to fa Talauci ne zai kashe su – Abdulwahab Bluelens

Babu wata hujja da za a dogara da ita cewa tallafi ba ya zuwa wajen Talaka wasu ne ke sacewa, man Fetur kaɗai ya isa misali a yanzu.
Karin N350 a kan kowacce Lita kudin taliya guda daya da Talaka zai saya ita ce zai saka a ƙarin kudin Mai, Wanda yake da Babur a kowacce rana zai sha mafi kankantar Mai na N1,100 lita (2) Mai hawa Mota kuwa N3,000 kullun.
Kowanne tallafi an cire shi na Man Fetur da na kananzir da Wuta da kuma na Ilmi, wai duk sabida wasu tsiraru ne ke amfana.
Tambaya itace idan har ba za su iya maganin su ba meye amfanin ku, sai dai mu kuyi maganin mu sabida mu ku ka Raina?
MATSALOLIN DA ZA A FUSKANTA.
1. ƘARUWAR RASHIN TSARO
2. MUMMUNAN TALAUCI
3. FASA SHAGUNA DA TARE MOTOCIN DAKE ƊAUKO KAYAN ABINCI
4. ƘARANCIN AIKIN YI
MAFITA.
Tilastawa gwamnoni da ƴan Majalisu su haskawa gwamnatin tarayya matsalar da ake ciki da kuma nunawa shugaban ƙasa kin amincewar su da wannan tsarin.
Idan kuwa gwamnoni da ƴan majalisu suka yadda da wannan tsarin haƙiƙa za su fuskanci matsaloli kala kala daga al’ummar da suke wakilta.
Ba Hujja bace idan anyi Campaign da Wani ƙudiri kuma bayan an fara aiwatar da shi aka ga al’ummar da za a yiwa za su shiga damuwa sai a dakatar a kuma janye a sake tunani.