Labarai
Tajuddeen Abbas ya bayyana sauran shugabanin majalisa

Shugaban Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas, ya bayyana Usman Bello Kumo na jam’iyyar APC daga Gombe, da Aliyu Sani Madakin Gini na NNPP daga Kano cikin ƙunshin jagororin majalisar.
Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo a matsayin mai tsawatarwar ɓangaren masu rinjaye.
Sai Aliyu Sani Madakin Gini a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Jaridar Solacebase, ta ruwaito cewa, Sauran jagororin da shugaban majalisar ya bayyana a ɓangaren masu rinjaye sun haɗa da Julius Ihonvbere a matsayin shugaban masu rinjaye da Abdullahi Halims mataimakinsa, Sai da Adewumi Onanuga mataimakin mai tsawatarwa.
A ɓangaren marasa rinjaye kuma, ya sanar da Kingsley Chinda a matsayin shugaba sai Ali Isa mai tsawatarwa da George Ozodinobi mataimakin mai tsawatarwa.