Labarai
Katsina: Ƴan sanda sun cafke mutane 8 bisa zargin ƙone musu mota

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ta ce, ta cafke wasu mutane takwas bisa zargin su da ƙone motar sintirin jami’an rundunar a garin Katsina.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ta cikin sanarwar, rundunar ta ce, bayan zargin ƙona motar kuma ta na zargin mutanen da laifin taimaka wa wani mutum da ya karya dokar hanya ya tsere.