Labarai
A Wata Ziyarar Ba Zata Zulum Ya Tarar Da Babban Asibiti Cikin Duhu

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin wutar lantarki da rashin kyakkyawan yanayi a babban asibitin garin Gwoza.
Zulum wanda ya kai ziyarar aiki ta yini a Gwoza, ya kwana a garin da ke shedikwatar karamar hukumar Gwoza a kudancin Borno.
Gwamnan, wanda ya saba kai ziyarar ba-zata a cibiyoyin gwamnati a kokarinsa na gane wa idonsa abubuwan da ke faruwa, ya je asibitin ne da tsakar daren ranar Asabar.
Zulum ya zagaya domin tantance yanayin da asibitin ke ciki.
“Ba abin yarda ba ne a ce cibiyar kiwon lafiya mai matukar muhimmanci kamar wannan babban asibitin Gwoza an hana shi kayayyakin more rayuwa kamar wutar lantarki.
“Wannan yanayin yana lalata ingancin kulawar da ake ba marasa lafiya kuma yana kawo cikas ga ƙoƙarin kwararrun likitocin mu na kiwon lafiya.
“Ba mu zo nan don mu’amala da zargi ba, mun zo ne don nemo mafita. Babu wanda ya kawo min tsogwamin munanan yanayin wannan wurin.
“Ba zan wanke kaina ko karamar hukuma ba. Mu (dukkanmu) mun kasa samar da abin da ake bukata.
“Sai dai ina so na tabbatar muku (masu lafiya da sauran jama’a) cewa insha Allahu za mu gyara, za mu kyautata yanayin aiki a nan fiye da yadda yake a yanzu,” inji Zulum.
A wani mataki na sauya yanayin da ya gani, Gwamna Zulum ya ba da umarnin a gaggauta fara ayyukan gyare-gyare da za su hada da dawo da wutar lantarki a asibitin.
A halin da ake ciki Gwamna Zulum ya yaba da ma’aikatan jinya wadanda duk da halin rashin kyakkyawan yanyi da babban Asibitin ke ciki, sun kasance a wurin domin gudanar da ayyuka.
Zulum ya sanar da bayar da tukuicin kyauta ga dukkan ma’aikatan da suka sadaukar da kansu wajen fuskantar kalubalen aikin.